Tambuwal da Saraki za suyi danasanin komawa PDP


Aliyu Magatakarda Wamako, sanata dake wakiltar mazabar arewacin Sokoto a majalisar dattawa ya ce Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jiharsa da kuma sanata Bukola Saraki za suyi danasanin ficewa daga jam’iyar APC.

Kafin Tambuwal ya fice daga PDP, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki gwamnoni biyu da yan majalisu da dama sun rigaya sun fice daga jam’iyar APC mai mulki.

Wamakko ya yi magana akan sauya shekar a wurin wani taron gangami na nuna goyon baya ga shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma jam’iyar APC wanda aka gudanar a Sokoto babban birnin jihar.

Sanatan ya ce yaƙin siyasar 2019 ba wai tsakaninsa bane da Tambuwal face tsakanin jam’iya mai mulki da kuma matacciyar jam’iya (PDP).

“Yanayin siyasar Sokoto a yanzu ba wai tsakani na ne da gwamna Tambuwal ba face tsakanin APC a matsayin jam’iyar siyasa da kuma PDP matacciyar jam’iya,” ya ce.

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce sauya shekar ta Tambuwal ba zai shafi damar cin zaɓe da jam’iyar take da shi a jihar.


Like it? Share with your friends!

2
139 shares, 2 points

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *Allah Ya kara maku daukaka da nasara mai girma sanata, Allah Ya kara imani. Kan dogewa bisa tafarkin gaskiya da kishin talakawa.

You may also like