TAKAITATTUN LABARAI


Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmad ta amince da shawarar bankin lamuni na duniya IMF akan cire tallafin mai.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da zunzurutun kudi har miliyan N357 da aka fito dasu daga gidan Gwamna Abiola Ajimobi na Oyo domin a kai banki.

Sojoji sun kashe yan bindiga guda 23, sun ceto mutame 40 a jihar Zamfara.

Jam’iyyar APC ta sha alwashin daukar mataki akan wadanda suka bijire mata.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayar da umurnin a fitar da bayannan yadda majalisar ke kashe kudin ta dalla-dalla.

Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe.

Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen dake wakana a Najeriya.

Kungiyar kwadago ta kasa ta baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin wata ɗaya domin ya sanya hannu akan dokar karin albashi.

Jam’iyyar APC reshen jihar Yobe ta shawarci Sanata Ali Ndume ya hakura ya yi biyayya ga jam’iyya a kan zabin Ahmad Lawan domin kare afkuwar baraka a jam’iyyar.

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sun gama shirye-shirye tsaf na gabatar da dokar tsarin tazarar haihuwa a jihar Kano.

Rundunar sojin saman ta nuna bacin ranta a kan sarakunan gargajiyan Zamfara, inda ta bukaci su gabatar da shaidu a kan zargin da sukayi cewar mutanen gari jiragen hukumar ke kashewa.

Tarayyar Turai ta bayyana cewar sojojin Sudan ba za su iya biyan bukatar al’umar kasar ba, a saboda haka su gaggauta mika wa farar hula mulki.

Rahotannin farko da aka samu na cewa, mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon wani bam da ya fashe a wata kasuwa dake garin Ketta na kasar Pakistan.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like