Takaddama kan kudin motocin ′yan majalisa | Labarai | DWTakaddama ta kaure a kasar Yuganda, bayan da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni, ta raba ma ‘yan majalisan kasar sama da dala miliyan talatin don siya musu motoci. Kowanne daga cikin ‘yan majalisan kasar da suka haura dari biyar, ya sami akalla dala dubu hamsin da shida a farkon wannan makon.

Masu sukar matakin gwamnatin, sun baiyana damuwa kan halin da kasar ta ke ciki na karancin allurar riga-kafin corona a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazana daga sabon nau’in corona mai suna Delta a zagaye na biyu. 

Wasu na zargin gwamnati da yin almubuzurranci da kudadenm kasa. Suna cewa, babu wani mataki, na a zo a gani, da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni ta dauka na dakile cutar, baya ga ayyana dokar kulle, kasar na ci gaba da fama da karancin kayan aiki a asibitoci da suka cika makil da masu fama da corona, a yayin da sauran al’ummar kasar ke kukan karancin kayayyakin kare kai daga kamuwa da cutar mai kama numfashi.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.