Surikin Rochas ya samu tikitin takarar gwamna a APC


Uche Nwosu, sirikin gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha shine mutumin da ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyar APC.

Ibrahim Agbabiaka, shugaban kwamitin shirya zaben shine ya sanar da haka inda ya ce Nwosu ya samu ƙuri’u 269524 da suka bashi nasarar cin zaben.

Wannan ne dai karo na biyu da ake sake gudanar da zaben bayan wanda aka yi inda shugaban kwamitin zaben Ahmad Gulak ya sanar da sanata Hope Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben.

Amma kwamitin zartarwar jam’iyar na kasa ya rusa kwamitin tare da kafa wani sabo da zai gudanar da jam’iyar.

Har ila yau Agbabiaka ya sanar da gwamnan jihar, Rochas Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na dantakarar sanata da zai wakilci mazabar.


Like it? Share with your friends!

-1
70 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like