Sunday Igboho ya fara shirin korar Fulani daga Ogun


Sunday Igboho, mSutumin da ya tunzura mutanen garin Igangan a jihar Oyo har suka kori Fulani makiyaya daga garin ya kai ziyara jihar Ogun a kokarin da yake na tabbatar da cewa an fatattaki fulani daga jihohin Yarabawa.

Tauraruwar Igboho ta fara haskakawa ne tun bayan da ya kai ziyara garin na Igangan inda hakan ya jawo a kona gidan sarkin Fulanin garin tare da kashe wasu mutane.

Tun daga wancan lokacin ne ya ci alwashin raba yankin kudu maso yammacin Najeriya da abun da ya kira Fulani makiyaya dake aikata laifi.

A yanzu dai za a iya cewa ya fara cika alkawarin da yayi bayan da aka ga wasu hotunansa dake nuna cewa ya isa jihar Ogun.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

You may also like