Sojojin sun ceto mutane da aka yi garkuwa da su a Borno


Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane uku da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Rundunar ta ce an ceto mutanen ne a kauyen Firgi dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin mai dauke da sahannun,Aminu Iliyasu.

Iliyasu ya ce an ceto mutanen ne sakamakon bayanan sirri da suka samu inda suka tsare yan ta’addar da har ta kai ga musayar wuta.

Ya kara da cewa sojojin sun kuma samu nasarar kwance bom da aka dana akan hanyar Bitta-Yamteke dake jihar.


Like it? Share with your friends!

-1
72 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like