Sojojin Nijeriya Sun Samu Gagarumar Nasara Akan Wasu ‘Yan Ta’ada A Jihar Zamfara


Hadin gwiwar rundunar sojoji masu yaki da muggan laifuka sun samu gagarumar nasara akan wasu ‘yan ta’adda masu zalunta al’umma wadanda ba su yarda da sulhu ba.

A ranar 21/11/2020 a yankin Galadi da ke cikin karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, jami’an sojoji sun halaka ‘yan ta’adda biyu tare da samun bindigogin su biyu kirar AK 47.

Haka kuma a yankin Sabon Tunga da Tamuske, jami’an tsaron sojin sun hallaka ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da mutane uku da suka yi garkuwa da su. A garin Dutsen Emai sojojin kundumbala sun hallaka ‘yan bindiga da dama ta hanyar amfani da jirgin yaki.

Ranar 21/ 11/ 2020, runduna sojoji a garin Gobirawa ta kara samun nasarar hallaka ‘yan bingiga 6 tare da samun bindigogi hudu kirar AK 47, da bindigar gargajiya 3 da babur biyu.

A garin Kadauri da ke cikin karama Hukuma Maru, Jihar Zamfara, jami’an tsaron sojojin sun kama mutane 11 da ake zargin su da aikin hako ma’adanai ba’a bisa ka’ida ba, tuni dai sojoji su ka mika su ga hukumar da ta dace dan bincike.

Jami’an tsaron sojoji da ke aiki a garin Kotarkoshi da ke cikin karamar hukumar Bungudu ta Gabas, sun yi nasarar cafke wani da su ke nema ruwa jallo mai suna Shafiu Suleman a cikin kasuwar garin. Bincike ya nuna yana da hannu a cikin wasu hare-hare da yankunan suka yi fama da su a kwanan baya.

Hakan ta sake faruwa a Gidan Ruwa kusa da Rukudawa da ke Zurmi, jihar Zamfara, ranar 22/11/ 2020, jami’an tsaron soji sun kai samame a yankin. Inda ‘Yan bindigar suna hango sojoji zuwa sai suka ranta a cikin na kare, duk da haka sojoji sun yi amfani da dubarun yaki sun hallaka dan Bindiga daya tare samun bindigar sa, AK 47 daya hadi da kama 2 daga cikin su.

A garin kurfi da ke cikin jihar Katsina, ranar 22 11/ 2020, jami’an tsaron sojin sun yi nasarar kame wani shugaban ‘yan ta’adda.

Kamar yadda Maj. Gen. John Enenche
Shugaban watsa labarai na rundunar sojoji ta kasa ya bayyana.

Allah ya kara bamu Zaman lafiya.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like