Sojojin Chadi na cigaba da ragargazar Boko Haram


Tun bayan da mayakan Boko Haram suka kashe sojojin kasar Chadi kusan 100 shugaban kasar,Idriss Derby ya ci alwashin fatattakar yan ta’addar kungiyar ta Boko Haram daga kasarsa.

Shugaban kasar shike jagorantar farmakin da sojojin kasar suke kai wa kan mayakan na Boko Haram.

Rahotanni dake fitowa daga kasar na nuni cewa tabbas kasar ta Chad na samun gagarumar nasara a yaki da Boko Haram.

Wasu fefayen bidiyo da kuma hotuna dake yawo a soshiyal midiya sun nuna irin nasarorin da dakarun na Chadi suka cimma.

Kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta wallafa wasu hotuna dake nuna tarin makaman da sojojin Chadi suka kwace daga hannun Boko Haram


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like