Wasu bayanai na nuna cewa gwamnagtin Amirka ta kashe kudi sama da dala tiriliyon biyu kan sojojinta da ke Afganistan, tun bayan da suka yi mamaya a shekarar 2001 bayan harin ta’addanci na 9 ga watan 11 a kasar Amirka.

Sai dai janye sojojin na zuwa ne a dai-dai lokacin da adadin mutanen da suka mutu a  sabon harin bam a masaukin baki da ke gabashin kasar ya karu zuwa 21, wasu 90 sun jikkata. Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin ko harin yana da alaka da fara ficewar sojojin Amirka daga kasar.