Dakarun gwamnatin Afghanistan sun kwace yankin iyakar kasar mai muhimmancin da kasar Pakistan daga hannun tsagerun kungiyar Taliban masu dauke da makamai. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito halaka mai daukan hoton kamfanin a yankin.

Mako guda da ya gabata ‘yan Taliban suka kwace yankin iyakar. Shaidun gani da ido daga bangaren Pakistan sun bayyana irin dauki ba dadin da aka tafka tsakainin bangaren biyu gabanin samun nasarar dakarun gwamnatin Afghansitan na sake kwace yankin mai tasiri.

Tun lokacin da aka bayyana kudirin janye dakarun kasashen duniya daga kasar ta Afghanistan bayan shafe kimanin shekaru 20, ‘yan Taliban suke amfani da damar wajen sake kwace yankuna da dama daga dakarun gwamnati.