Sojoji a kasar Gabon sun kwace mulki daga hannun shugaban kasar Ali Bongo.

Kafar yada labarai ta BBC ta rawaito sojojin na cewa sun kwace mulki ne domin dawo da kasar kan turbar dimakwaradiya.

Sun kwace iko da gidan radiyon kasar da safiyar ranar Litinin inda suka karanta wani takaitaccen sako.

Kafar ta BBC ta bayyana cewa an girke tankokin yaki da kuma motocin sulke a titunan Liberaville babban birnin kasar.

A yanzu haka dai shugaban kasar na can na jiya a kasar Saudiyya bayan da ya gamu da cutar shanyewar barin jiki a cikin watan Oktoba.

Bongo ya karbi mulki a shekarar 2009 bayan rasuwar mahaifinsa.