Sojoji Sun Kewaye Gidan Nnamdi Kanu 


Sojojin Najeriya sun zagaye gidan Nnamdi Kanu   jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, dake Umuahia babban birnin jihar Abia.

Kasancewar sojoji a garin da Nnamdi Kanu yake, sau biyu kenan cikin kwanaki uku inda suka yi fada da magoya bayansa a ranar Lahadi.

An rawaito cewa sojojin sun isa gidan a ranar Talata cikin motocin sulke da kuma Toyota Hilux.

Wasu daga cikin sojojin sun isa ofishin kungiyar yan jaridu ta kasa NUJ dake  Umuahia.

Kayayyaki na miliyoyin naira da suka hada Laptop suka lalata a sakatariyar.

Sai dai sojojin sun yi zargin cewa sun ga wanine yana daukarsu a hoto daga cikin ginin sakatariyar.

John Emejor shugaban kungiyar ta NUJ a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sojojin sun mari daya daga cikin shugabannin kungiyar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like