Sojoji sun kashe wata yar kunar bakin wake a jihar Adamawa


Rundunar sojan Najeriya tayi nasarar kashe wata mata mai shirin kai harin kunar bakin wake a wani wurin binciken ababen hawa dake garin Gulak na jihar Adamawa.

Rundunar sojan ta bayyana haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

A cewar sanarwar sojojin da suka fito daga Bataliya ta 143 wadanda aka jibge a shingen binciken sune suka samu nasarar kashe matar wacce take sanye da rigar bam.

Matar tayi kokarin shiga kauyen DAR domin tayar da bom din dake jikinta.

Harin kuna bakin wake da yan mata suke kai wa abune da ya zama ruwan dare a yankin arewa maso gabashin Najeriya dake fama da rikicin Boko Haram.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like