Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram uku


Yan ta’addan da basu gaza uku ne ba sojojin Najeriya suka kashe lokacin da suka yi kokarin kai hari kan ayarin motocin yan gudun hijira dake komawa Baga daga Maiduguri.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Najeriya, John Enenche shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar ta samu nasarar kwato wasu makamai da kuma harsashi.

Enenche ya ce rundunar sojan ta kuma samu nasarar kama wani mai garkuwa da mutane tare da satar shanu a kauyen Takum dake karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Har ila yau rundunar ta kama wasu masu garkuwa da mutane da suka hada da Yahaya Muhammad dake kauyen Zalau a karamar hukumar Toro sai kuma Juli Ardo dake kauyen Lariki a karamar hukumar Kirfi a jihar Bauchi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 10

Your email address will not be published.

You may also like