Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan boko haram sama da 20 tare da kwace makamai da dama ciki har da wasu motoci dake dauke da bindiga.

A ranar 12 ga watan Disamba ne sojojin suka samu gagarumar nasara akan yan ta’addar kungiyar ta Boko Haram bayan da suka yi kokarin kai hari garin Askira Uba dake jihar Borno.

Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta bayyana cewa ana kyautata zaton mayakan na Boko Haram sun fito ne daga dajin Sambisa inda suka farma garin ta …ďangarori da dama.

Sanarwar ta ce motoci dake dauke da bindiga guda hudu aka samu nasarar kwacewa.

Har ila yau jami’an sojan sun samu nasarar kwato babur kirar Bajaj guda uku da wasu kayayyakin yaki da dama.