Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 7 a Borno


Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram bakwai a garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

Wasu majiyoyi ne suka tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa mayakan sun shiga garin cikin motoci 13 dake dauke da bindiga a ranar Alhamis inda suka yi kokarin kai farmaki sansanin sojoji.

Sojojin sun samu nasarar dakile harin abin da ya tilastawa mayakan na Boko Haram tserewa.

Wani yaro dan shekara biyar ya ransa a harin sanadiyyar musayar wuta.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like