Sojoji sun kashe masu tada kayar baya 23 a yankin Tafkin Chadji


Rundunar sojan Najeriya ta kashe ya’yan kungiyar Boko Haram 23 tare da kwato makamai a farmakin da take cigaba da kai wa a wasu kauyuka dake yankin Tafkin Chadji.

Jude Texas Chukwu, daraktan hulda na rundunar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

Ya ce da yawa daga cikin yan ta’addar sun tsere da raunin harbin bindiga ya yin arangamar da suka yi da sojojin ranar Litinin.

Chukwu, ya ce sojojin bataliya ta 153 tare da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar Kamaru su ne suka kai farmakin.

Ya lissafa kayan da aka gano da suka hada da bindiga kirar Ak-47 guda shida, bindiga biyu samfurin NR, baburan hawa biyu, harsashai da kuma gidan zuba harshin bindigar AK-47 guda takwas.

Ya kara da cewa tun farko sojoji sun samu nasarar kakkabe yan ta’addar daga kauyukan, Bulakeisa, Tumbuma Babba, Abbaganaram and Dan Baure dukkanninsu dake yankin na Tafkin Chadji.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like