Sojoji sun kashe barayi 23 a Zamfara


Sojoji dake gudanar da yaki da barayi da kuma masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun kashe barayi 23 tare da kama wasu mutane 18 dake samar da bayanai, ga yanbindiga,barayin shanu, masu garkuwa da mutane da kuma masu samar musu da kayan amfanin yau da kullum.

Mai rikon mukamin jami’in yada labarai na rundunar Operation Sharar Daji,Manjo Clement Abiade shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce bangaren sojan sama na rundunar ya kai hare-hare ta sama da dama a wajen Kagara, Gandi,Fankama, Fete da kuma dajin Dumburum.

Har ila yau an kama wani rikakken mai garkuwa da mutane mai suna, Muhammad Iso a kasar jamhuriyyar Nijar ta hanyar hada kai da jami’an tsaron kasar.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar ta samu nasarar ceto mutane 40 da suka kunshi maza, mata ,yara da wadanda aka sace daga garuruwa daban-daban na jihar ta Zamfara


Like it? Share with your friends!

-1
56 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like