Sojoji Sun Kama Wasu ‘Yan Boko Haram Da Ake Nema Ruwa A Jallo


Dakarun sojojin kundunbala na Nijeriya da hadin gwiwar mayaka ‘yan sa kai Civilian JTF reshen karamar hukumar Bama a jihar Borno, sun samu nasarar farautar wasu fitinannun ‘yan ta’addan Boko Haram har da wadanda ake nemansu ruwa a jallo.An kama ‘yan ta’addan ne a yankin garin Gwoza wani kauye da ake kira Pulka, ‘yan ta’addan suna shigowa cikin gari su sayi abinci sannan su koma jeji, sun zo sun sayi abinci akan hanyar su na komawa jeji sai aka bi diddiginsu aka musu kofar rago aka kama su.Muna rokon Allah Ya tabbatar da nasaran jami’an tsaron Kasarmu Nigeria akan annoba ‘yan ta’addan Boko Haram da masu tallafa musu ta kowace irin hanya. Amin.


Like it? Share with your friends!

-1
77 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like