Sojoji sun kama mutane biyu dake da hannu a kashe-kashen jihar Taraba


Sojojin Najeriya dake gudanar da atisayen ‘Ayem Akpatuma’ da ake yi domin kakkabe batagari daga wasu jihohin kasarnan, sun kama wasu mutane biyu dake da hannu a kisan mutane da kuma tashin hankalin dake faruwa a kananan hukumonin Takum da Ussa a jihar Taraba.

Mutanen da aka kama a jiya sun hada da Danasabe Gasama da kuma Mista Danjuma wanda aka fi sani da Amerikan.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ce mutanen biyu da ake zargi an kama su ne a Takum bayan wasu bayanan sirri dake nuna cewa su ne suka shirya wasu hare-hare akan fulani makiyaya da ma yan gari.

Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen kashe-kashe da kuma tashin hankalin dake faruwa a kananan hukumomin biyu

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like