Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri


A daren ranar Litinin ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai farmaki kan wani sansanin sojoji dake Maiduguri.

Amma kuma jami’an soja sun samu nasarar dakile harin ta hanyar fatattakar yan bindigar bayan musayar wuta ta tsawon lokaci.

Bayanan da jaridar ta tattara sun nuna cewa sun kai hari kan unguwannin Aji da Kofa dake bayan rukinin gidajen 777 dake kusa da barikin sojoji ta 333 Atileri dake Maiduguri da misalin karfe 08:20 na dare.

A cewar majiyar jami’an tsaro yan ta’addar sun yi yunkurin kai hari ne barikin sojojin amma suka fuskanci turjiya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like