Sojan saman Najeriya na gab da kammala daukar horo kan jiragen yakin Super Tucano


Gabanin kawo sababbin jiragen yaki samfurin Super Tucano da Najeriya ta saya daga kasar Amurka a yanzu haka sojojin saman na Najeriya na gab da kammala samun horo kan yadda za su sarrafa tare da kula da jiragen.

Sojojin na samun horon ne a kasar Amurka.

Idan mai karatu zai iya tunawa a shekarar 2021 aka yi alkawarin kawo jiragen Najeriya.

Masharhanta kan lamarin tsaro na ganin jiragen za su taimaka matuka a yakin da jami’an tsaro suke da mayakan Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 5

You may also like