Sojan ruwa a Akwa Ibom sun kama masu fasa kaurin shinkafa daga kasar Kamaru


Dakarun Sojan Ruwan Najeriya a jihar Akwa Ibom sun kama wasu mutane shida tare da kwace buhuna 416 na shinkafar da aka haramta shigowa da ita daga hannun mutanen.

Da yake magana a Ibaka a wurin mika mutanen da ake zargi tare da shinkafar ga hukumar kwastam ta Najeriya kwamandan sansanin rundunar sojan ruwan dake Ibaka a karamar hukumar Ibaka Mbo, Kaftin Toritseju Vincent ya ce rundunar sojan ruwan za ta cigaba da iya bakin kokarinta wajen kawo ƙarshen fasa kwaurin shinkafa.

Kwamandan shiya na hukumar ta kwastam,Kolade Iloyede shine ya karbi mutanen da ake zargi tare da shinkafar daga sojan ruwan inda ya yi alkawarin gurfanar da su gaban shari’a su fuskanci hukunci domin haka ya zama izina ga masu aikata haka.

Daya daga cikin mutanen da ake zargi,Abia Etim ya musalta cewa yana da hannu a fasa kaurin inda ya ce shi fasinja ne kawai a cikin jirgin da aka kama bayan da ya hawo jirgin daga kamaru zuwa Najeriya.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like