Soja ya harbe kansa a yankin arewa maso gabas


Wani soja dake rundunar dakarun dake yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ya kashe kansa. The

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sojan mai muƙamin kofural na aiki ne da dakarun dake Buni Gari a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe kuma ya kashe kansa ne a ranar Alhamis.

Kawo yanzu ba’a san dalilin da yasa ya aikata haka ba sai dai wata majiya ta ce sojan kawai ya dauki bindiga ne inda ya harbi kansa a aka.

“Ya harbi kansa a kai kuma ya mutu nan take kafin ma sauran dakarun su garzaya su kawo masa dauki.”a cewar wata majiya ta soja.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like