Soja ya dawo gida ya samu matarsa da tsohon juna biyu bayan ya shafe fiye da shekara a Borno


Wani sojan Najeriya ya bayyana bacin ransa bayan ya dawo gida ya samu amaryarsa dauke da tsohon cikin da tsohon saurayinta ya yi mata lokacin da aka tura shi yaki da Boko Haram a jihar Borno, inda ya shafe watanni takwas.

A hirar da sojan ya yi da abokinsa, wacce wata kafar yada labarai (Gistvic) ta watsa, sojan ya ce ya yanke shawarar mayar da amaryarsa garinsu domin ta zauna tare da mahaifiyarsa bayan an tura shi jihar Borno.

Sai dai, matar Sojan ta koma cin soyayyar ta da tsohon saurayinta da ke kauyen musamman ganin cewa an dauki tsawon watanni ba tare da yin ko waya da mijin nata ba.

Yace ” Ta dauka na mutu ne saboda mun dauki tsawon watanni 8 ba muyi waya ba, sai kawai ta koma wurin tsohon saurayinta suka cigaba da soyayya, har ta kai ga ya yi mata ciki .

” Kuma wani abun haushi ma shine, ita ce ke fada min cewa kar na ga laifinta, na ga laifin aikin soja. Saboda karfin hali ma, tambaya ta tayi wai ita itace ce da zata zauna tsawon wata shida ba tare da wani ya taba ta ba, ” kamar yadda soja ya fada wa abokinsa a cikin hirarsu.

Sai dai, shi da kansa abokin sojan ya bashi shawarar cewa ya yi hakuri ya cigaba da zamansa da matar a haka, saboda ta aikata hakan saboda rashinsa a kusa da ita.

Me za kuce akan hakan?

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like