Soja daya da kuma wasu mutane 9 sun mutu a ambaliyar ruwa a jihar Kebbi.


Gwamnatin jihar Kebbi a ranar Talata ta tabbatar da mutuwar wani soja guda daya da kuma wasu mutane 9 a wata ambaliyar ruwa biyu da aka yi a jihar.

A wata sanarwa da aka fitar a birnin Kebbi mai dauke da sahannun, Abubukar Dakingari jami’in yada labaran gwamnan jihar, Atiku Bagudu, ya ce ambaliyar ruwan ta faru a kananan hukumomi biyu dake jihar.

Dakingari ya lissafa kauyukan da abin ya shafa da suka hada da kauyen Kanya a karamar hukumar Danko Wasagu da kuma kauyen Mahuta a karamar hukumar Fakai.

Ya ce ” wani soja da kuma wasu mutane sun rasa rayukansu a mamakon ambaliyar ruwa sakamakon yawan ruwan sama a jihar an ce sojan ya mutu ne lokacin da yake kokarin ceto wata mace daga ambaliyar ruwan.

Dakin gari ya ce duk da an samu nasarar samun gawar matar amma ruwa ya tafi da gawar sojan.

Ya kara da cewa mutane biyar ne suka mutu a kauyen Kanya, uku kuma a Mahuta.


Like it? Share with your friends!

-1
90 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like