SIYASAR DABA A JIHAR KANO


Kusan tun lokacin da aka fara yakin neman zabe a jihar Kano ake kisa da sara-suka gami da kwace. Kamar yadda a baya Boko Haram suke kai hari da rana tsaka a Maiduguri kowa na gani, haka yanzu a jihar Kano bayan taro ‘yan daba dauke da makamai suke yawo a jihar Kano.

Lungu da sako da kowane Kwararo haka za su biyo suna sara gami da kwacen waya da lalata abubuwa.

Mutane da dama da ba su ji ba su kuma gani ba sun gamu da tsautsayi Daban-daban bayan kammala yakin neman zabukan siyasa.

Allah Yana gani zai kuma yi hukunci, duk wanda ya zama silar kisan ran Musulmi da gangan Allah da Mala’iku sun la’ance shi kuma wutar Jahannama ce makomar sa.

Duk wanda ya ba ka makami don ka kashe wani uban wani ya ci zabe ko shi ya ci zabe, Wallahi sai Allah Ya wulakanta ku Ya kaskantar da Ku.


Like it? Share with your friends!

1
42 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like