Shugabannin Igbo sun bukaci a hukunta wadanda suka sace yaran Kano 9


Shugabannin al’ummar Igbo mazauna Kano sun ce wadanda suka sace yara a Kano tare da fataucinsu zuwa yankin kudu maso gabas dole ne su fuskanci hukunci.

A makon da ya wuce rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutane 8 da ake zargi da kwarewa wajen sacewa tare da sayar da kananan yara.

Yara 9 ne dai ake zargin an sace su a Kano, jami’an yan sanda suka ceto a jihar Anambra.

A wata sanarwa ranar Laraba,Ebenezer Chima shugaban kungiyar al’ummar Igbo mazauna Kano da Boniface Ibekwe sarkin kabilar Igbo sun yi allawadai da abinda mutanen suka aikata.

Sun yi kira ga yan sanda da su hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Shugabannin biyu sun yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II kan hanyar da suka bi wajen kula da lamarin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like