Rahotanni daga Jihar Kaduna sun tabbatar da cewar Shugabannin riƙon Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna sun kira wani taron gaggawa don yima Kakakin Majalisar Jihar Kaduna Yusuf Zailani, gargadi kan sukar Sanata Mai wakiltar Jihar ta tsakiya Sanata Uba Sani.Rahotan hakan na kushe cikin wata takardar bayan taro da Shugabannin suka fita jim kadan bayan kammala taron gargadin.


Sun kira hakan da rashin daraja na gaba tare da rashin daraja Jam’iyya daya, har ma sun zargi hakan da yima Jam’iyya makarkashi.


Sun kara da cewa suna cike da abun mamaki ganin cewa jagora mai muƙami na 3 a jiha Kamar Kaduna yana irin wadannan maganganun, sun ce wannan kuskure ne; inji su.

Shugabannin Jam’iyyar kananan Jihar Kaduna ta tsakiyar da suka hadar da Igabi da Kaduna North da Kaduna South da Birnin Gwari da Chikun da kajuru da kuma Karamar Hukumar Giwa.

Kunshe cikin bayanin lokacin da yake zantawa da wakilin mu Shuaibu Abdullahi ta wayar tarho Honorabul Gambo Shehu Haske, ya tabbatar da cewar Sanata Uba Sani, ya kai kololuwa wajen bayar da gudun-mawa a tarihin kujerar Sanatan Jihar Kaduna ta tsakiya kuma Karamar hukumar Igabi da Zailani ya fito ta fi amfana da dukkan tsare-tsaren cigaba da Sanata ya zo da shi.

Yanzu haka sun aike da rahoto ga Uwar Jam’iyyar APC ta kasa don daukar matakan da suka dace.

Ko kadan ba zasu lamunci irin wadannan dabi’un ba daga karshe Sun yi gugar zana tare da yin barazana a kaikaice ga Zailani.