Shugaban NNPC ya roƙi dillalan mai da kada su tsunduma yajin aiki


Maikanti Baru, shugaban Kamfanin mai na kasa NNPC, ya shawarci kungiyar dillalan mai masu zaman kansu ta kasa IPMAN da kada su tsunduma yajin aikin da suka shirya yi.

Baru yayi wannan kiran ne a lokacin da yake buɗe gidan man NNPC a garin Shagamu na jihar Ogun.
Reshen  Kungiyar ta  IPMAN, a jihar Lagos ta zargi NNPC da laifin saba alkawarin sayar masu da mai kan naira 135 kan kowacce lita.
Kungiyar tace sun shirya saka kafar wando ɗaya da NNPC kan rashin samar da mai akai-akai a wajen ajiye mai dake Ejigbo.
Da yake mai da martani, Baru yace wannan ba lokacin da yadace bane da yayan kungiyar zasu tsunduma yajin aiki.

A cewarsa  kamfanin mai nakasa shine kamfani daya tilo da yake shigo dan mai kuma yana sayar dashi a farashin da hukumar kayyade farashin man fetur ta amince a sayar na ₦135 kan kowacce lita.
Ya ce babu wani dalili da zai saka dillalan su sayar da litar mai kan kuɗi sama da ₦145.

Ya shawarce ya’yan  kungiyar ta IPMAN da su kai rahoton duk wani babban dillali dake sayar dan man kan kuɗi sama da ₦141 ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar mataki.

 


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like