Shugaban kasar Sudan ya bada umarnin sakin dukkanin fursunonin siyasa


Shugaban kasar Sudan, Omar Hassan Al Bashir ya bada umarnin sakin dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a gidajen yarin ƙasar.

A cewar wasu rahotanni, matakin na zuwa ne a matsayin wani martani kan kiran da jam’iyun siyasa da wasu kungiyoyi suka yi,dake halartar taron tattaunawa na kasar dake gudana a kasar na abawa mutanen da ake tsare da su damar shiga a dama da su a harkokin siyasar kasar.

Karkashin shirin tattaunawar Bashir ya gana da yan adawa da kuma kungiyoyin yan tawaye, tun daga shekarar 2015 ya zuwa yanzu.

Amma kungiyoyi da dama sun kauracewa shirin inda suka bukaci Bashir da ya fara yin gyara kan dokokin tsaro da kuma wasu dokoki dake musgunawa yan Jaridu.

A cikin watan Maris, Bashir ya yi umarni da a saki fursunonin siyasa su 80 mako guda da kama su bayan wata zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar kan tsadar kayan abinci da kuma matakin gwamnati na tsuke bakin aljihu.

Kungiyoyin adawa, sun ce kusan fursunonin siyasa 50 ake cigaba da tsare su a gidajen yari da suka haɗa da fitaccen dan siyasa Mohamed Mokhtar al-Khatib, wanda shine shugaban jam’iyar kwaminisanci ta kasar Sudan.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like