Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara hakan man fetir a jahar Gombe


Rahoton dake shigo mana da dumi duminsa na nuni da cewar, a yau Asabar, 2 ga watan Janairu,shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara hako man fetur a jihar Gombe, wanda hakan zai shigar da jahar Gombe cikin jerin jihohin Najeriya dake da arzikin man fetir.

Majiyarmu ta ruwaito shugaba Buhari zai kaddamar da hakan man ne a yankin tafkin Kolmani, wani sashi dake tsakanin jahar Gombe da jahar Bauchi, kamar yadda hukumar man fetir na Najeriya, NNPC ta sanar.

Babban manajan watsa labaru na hukumar NNPC, Ndu Ughamadu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, inda yace shugaba Buhari zai kaddamar da aikin ne tare da hadin gwiwar shugaban NNPC, Maikanti Baru.

Yankin da za’a kaddamar da hakan man fetir din, tafkin Kolmani II, yana kusa da kauyen Barambu dake cikin karamar hukumar Alkaleri na jahar Bauchi, haka zalika Mista Ndu yace an soma hakan man fetir dinne sakamakon wasu sabbin dabaru da shugaban NNPC, Maikanti ya zo dasu.

Makasudin samar da wadannan dabaru shine domin kara adadin danyen mai da iskar gas da Najeriya take fitarwa, samar da isashshen man fetir a Najeriya, samar da karin kudin shiga ga gwamnati da kuma samun karin wuraren hako mai a yankin Arewa.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like