Shugaban karamar hukumar Giwa ya sayawa jami’an tsaro motar sintiri


A kokarinsa na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna,shugaban karamar hukumar,Abubakar Shehu Giwa ya sayawa jami’an tsaro sabuwar motar sulke da su rika gudanar da sinitiri a ciki.

A makon da ya wuce ne a kona motar jami’an tsaro a wata arangama da suka yi da wasu barayi dake dauke da makamai.

Jami’an sun yi artabu da yan bindigar ne a yankin Galadimawa dake jihar.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like