Shugaban jam’iyyar Labour Party (LP),Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ya rasu.

Mai magana da yawun IPAC wacce kungiya ce ta hadakar jam’iyyun siyasar Najeriya, Major Agbo ya tabbatarwa da jaridar Dailiy Trust ra rasuwar shugaban jam’iyyar ta LP.

Shima Dr. Yunusa wanda tsohon shugaban kungiyar ta IPAC ne ya tabbatar da rasuwar marigayin.

Tuni aka gudanar da jana’izar marigayin a babban masallacin Minna da karfe biyar na yamma.