Dogaran da ke kula da tsaron Emmanuel Macron sun kama wasu matasa biyu ‘yan shekaru 28 da haihuwa da ake zargi da aikata da laifin marin shugaban Faransa, in ji ofishin mai gabatar da kara. Shugaban Macron ya ziyarci wata makarantar sakandare na garin Tain-l’hermitage, kafin ya taka zuwa wurin da ‘yan garin da suka zo yi masa marhabin da lale, a lokacin da lamarin ya faru. 

Shi dai Mista Macron yana “rangadin yankuna na Faransa”  don sanin zahirin abin da kasa ke ciki bayan fiye da shekara guda da matsalar annobar corona. Shugabannin jam’iyyun siyasa sun yi Allah wadai da abin da ya faru, wanda ya zo a daidai lokacin da zaben shugaban kasa na 2022 ke dada karatowa.