Shugaba Buhari Ya Jinjinawa ‘Yan Nijeriya Wadanda Suka Kau Da Kai Game Da Kiraye-kirayen Zanga-zangar Juyin Juya Hali


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa milyoyin ‘yan Nijeriya wadanda suka kau da kai daga kiraye-kirayen da aka rika yi a shafukan sada zumunta akan su fito zanga-zangar juyin juya hali, amma suka ki fitowa suka ci gaba da harkokinsu.

Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja. Ya ce shugaban kasar ya ji dadin goyon bayan da aka baiwa tafiyar dimokradiyya a Nijeriya.

Ya ce duk da akwai wadansu daruruwan mutane wadanda a bisa cimma muradin kawukansu ne suka fita wannan zanga-zangar amma ba don manufar kasa ba.


Like it? Share with your friends!

1
135 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like