Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum, ya ce gwamnatin jiharsa ta nemi kudi daga hannun gwamnatin tarayya, a kan ginawa masu gudun hijira gidaje, kuma an basu kudin.
Gwamnan, ya yaba wa shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarinsa da jajircewarsa a kan sakin kudin gine-ginen gidajen ‘yan gudun hijira miliyan 1.7, wadanda ‘yan boko haram suka lalata.
Gwamnan yace kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar don gina gidaje 10,000 na a kalla ‘yan gudun hijira miliyan 1.7 da ya kamata a ce sun koma anguwanninsu aikin ya fara kan kama.