Shekau ya yi allawadai da hukuncin da hukuncin kisa da aka yankewa mawaki a Kano


Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi allawadai da hukuncin kisa da wata kotu dake Kano ta yankewa wani mawaki da ake zarginsa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu.

Cikin wani sakon murya da wallafa Shekau ya ce babu babbanci a tsakanin wanda ya yi batancin da kuma wadanda suka yanke masa hukuncin.

Kwanaki uku bayan yanke hukuncin kawo yanzu ana ci-gaba da ce-ce-kuce a kafafen sadarwar zamani kan dacewar yin haka ko kuma akasin haka.

“Mun samu labarin wani abun bakin ciki da yake faruwa a jihar da mutanenta suke tunanin su Musulmai ne duk da cewa suna bauta ba dai-dai ba,” ya ce

Ya kara da cewa Kano jiha ce ta kafirai bata musulunci ba inda ake gudanar da mulkin dimakwaradiya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like