Sheikh Nasirudeen Adam Funtua Ya Rasu Bayan Kammala Aikin Hajji A Saudiyya


Allah ya yi wa shahararren Malamin addinin musuluncin nan, na jihar Katsina, Sheikh Nasirudeen Adam Funtua, rasuwa a Makka, bayan kammala aikinsa na Hajjin bana.

Kafin rasuwar shi ne Limamin Juma’a na Masallacin Sabuwar Unguwar, Tudun Matawalle, Kofar Kaura Katsina. Haka kuma yana cikin Malaman da Gwamnatin jihar Katsina ta dauka, domin yin wa’azi ga Alhazai a kasa Mai tsarki.

Tsohan malamin Makarantar Horas Da Malamai Da Harshen larabci ta (ATC) Katsina. Shugaban kwamitin Malamai da jihar Katsina ta tura kasa Mai tsarki, Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya ya tabbatar da rasuwarsa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like