Shehu Sani Ya Nuna Goyon Bayan Sa Ga Yajin Aikin ASUU


Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya nuna goyon bayansa ga kungiyar malaman jami’a ASUU bisa yajin aiki na sai Baba ta gani da ta yi a shakaran jiya Lahadi.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ke nuna gamsuwa da goyon bayansa da kudirin ASUU na yanke hukuncin shiga yajin aiki, inda ya bayyana matsayin na ASUU a matsayin matakin farfado da jami’o’in kasar nan daga dogon suma da suka yi sakamakon muguwar shaka da gwamnati ta yi musu.

Shehu Sani ya rubuta: “Ina tare da ASUU kan batun yajin aikin da suka shiga, kuma na gamsu da yunkurinsu a matsayin wani kokari na farfado da jami’o’in kasar nan.”

“A yayin da a ke sayar da gangar man fetur akan dalar Amurka 70, Nijeriya na da karfin tattalin arzikin da za ta iya kulawa da jami’o’in kasar nan yadda ya kamata. Ya kamata masu ruwa da tsaki na kasar nan da ke ilimantar da ‘ya’yansu a kasashen waje, su yi wa kansu adalci.”


Like it? Share with your friends!

1
70 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like