SHAWARA GA MASU ZABE


1- Ka tabbatar Kuri’arka Amana ce da za’a tambayeka akan wa ka zaba? kuma me yasa ka zabe shi?

2- Ka Zabi wanda Zai tabbatar maka da Addininka da tsoron Allah da hana Fasadi, ka da ka taimake wanda zai bun kasa Sabon Allah da ketare iyaka.

3- Kada ka shiga cikin wadanda zasuyi bangan siyasa ayi Amfani da su, wajen zubar da jini da Lalata Dukiyar al’umma da sanya Firgici a zuciyar mutane.

4- Kada wani ya baka Kudi ko kayan maye dan ka biya masa bukatarsa a wannan yananyi.

5- Ka hana Yaranka, da abokanka shiga Bangar Siyaysa.

6- Ka bawa hukumomi hadin Kai tun daga Jami’an Tsaro da hukumar zabe, a samu nasarar yin zabe lafiya.

7- in wanda ka zaba ya samu Nasara, kayi godiya ga Allah ta hanyar da Allah yaso ya yarda dashi, kada ka fito Celebration ta hanyar Wasa da ababawan hawa.

8- in naka bai ci ba, kayi Istirja’i da addua Allah ya sa haka shine mafi Alheri.

9- Musulunci baya goyon bayan zagin shugabanni da la’antar su, Addua ake masu Allah ya taimake su.

10- Muyi ta Addua Allah Ya zaba mana Shuwagabanni nagari.

#Copied


Like it? Share with your friends!

-1
39 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like