Shari’ar Maryam Sanda: Shekara Daya Bayan Kisan Bilyaminu, An Nemi Mai Bada Shaida An Rasa A Kotu


Rashin mai bada shaida, Hussein Okpetu,a kotu ya hana karar Maryam Sanda da ake zargi da kisan mijinta cigaba a kotu.

Mr Hussein Okpetu ya kasance mutum na shida da zai bada shaida a kotu kan yadda aka kashe Bilyaminu.

Ana tuhumar Maryam Sanda ne da kisan Bilyaminu Bello, dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP,Halliru Bello.

An gurfanar da ita ne tare da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; dan uwanta, Aliyu Sanda; da mai aikin gidansu, Sadiya Aminu.

A ranar Litinin, lauyan gwamnati, Fidelis Ogbegbe, ya gabatar da Josephine Onyentu, domin bada shaida a kotu sakamakon rashin ganin Mr Hussein Okpetu Lauyan ya bayyana cewa an kawo wata daban ne saboda hukumar yan sandan Najeriya ta mayar da Hussein Okpetu jihar Ondo kuma aka maye gurbinsa da Mrs Onyetu, tunda mamba ce a kwamitin binciken.

Amma lauyan Maryam Sanda, Olusegun Jolawa, ya ce bai daidai bane a gabatar da mai bada shaida wanda babu sunansa cikin masu bada shaida.

Mr Jolawo ya ambaci sashe 379 na kundin tsarin mulki wanda yace wajibi ne duk mai bada shaida ya gabatar da hujja kafin bada shaida.

Lauyan gwamnati Mr Ogbegbe yace tunda lauyan gwamnati bai amince wata ta bada hujja a madadin Hussein Okpetu ba, yana bukatar lokaci domin tattaunawa da shi kan yadda zai halarci zaman kotu a ranar da alkali ya bada anan gaba.


Like it? Share with your friends!

1
114 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like