Sharhin Huɗubar Juma’a kan sakin aure.


Liman Abba Sulaiman Khalid

Sharhin huɗubar Juma’a daga masallacin juma’a na filin jiragen sama na Mallam Aminu Kano. 

Yau limamin masallacin malam Abba Sulaiman Khalid yayi huduba kan SAKI na aure, da farko ya fara da godiya da kirari ga Allah madaukakin sarki, da kuma salati ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W. Ya kawo hadisin da annabi S. A.W yake cewa “mafi ƙin halal a wajen ubangiji shine saki,” saboda kuwa gashi halal ne amma Allah yana ƙinsa, yayi bayani sosai kan hadisin.

Yace alkali ko sarki suna da ikon raba aure idan an kai ƙara gabansu, ko dai in ya kasance cutarwa daga matar ko daga mijin. Miji idan ya samu saɓani tsakaninsa da matarsa, to ya fara yi mata wa’azi, kuma ba da rana ba, ba gaban jama’a ba a’a da daddare ya lallaba, yayi mata magana ta hikima, ya nuna mata ya kamata su sulhunta, idan bata ji ba ya kaurace mata wajen kwana.

Ya cigaba da mu’amala cikin gidansa, kana ya sauke haƙƙin da yake kansa na ciyar da ita, idan hakan bai sa ta hakura ba to ya dake ta, amma dukan da hannun rigarsa, idan hakan ma bai yiwu ba, sai a kirawo waliyyanta da nasa, idan an turza daidaito bai yiwu ba to sai ayi saki, kuma idan anyi sakin guda daya to ta zauna a gidan ba zai mu’amalance ta ba har sai tayi tsarki uku, amma idan kafin ya kai ukun ma sai suka samu dai-daito sai ya dawo ya cigaba da mu’amala da ita.

Sannan idan har ya kai ta yi  tsarki uku basu samu dai-daito ba  to kuma sai yake so ya dawo da ita to wannan fa sai an sake sabon daurin aure.

 Liman ya kara da cewa idan mutum ya auri budurwa ko bazawara amma bai tara da ita ba kuma yayi mata saki uku, to wannan saki a matsayin saki ɗaya yake, amma idan ya tara da ita kuma yayi mata saki uku to ta haramta gare shi . Wannan a takaice kenan na abinda hudubar ta kunsa.

Sharhi daga dalibin Liman, Mallam Muhammad Sani.


Like it? Share with your friends!

-1
56 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like