SDP ta goyi bayan takarar Buhari


Jam’iyar SDP ta amince da shugaban kasa Muhammad Buhari a matsayin wanda za ta goyi baya a zaben shugaban kasa.

Jam’iyar ta cimma wannan matsaya ne ranar Alhamis a wurin taron shugabanninta na kasa data gudanar a Abuja.

Buhari shine dantakarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Kwamitin zartarwar jam’iyar na kasa ya ce hakan ba yana nufin hadewa bane da jam’iyar APC.

Kafin jam’iyar ta cimma wannan mataki, tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke shine keyi mata takarar shugaban kasa.

An ayyana Duke a matsayin dantakarar shugaban kasa bayan hukuncin da wata kotun daukaka kara dake birnin tarayya Abuja ta yanke na jingine hukuncin babbar kotun tarayya dake Abuja da ya ayyana Jerry Gana a matsayin dantakarar shugaban kasa a jam’iyar

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like