SDP ta dakatar da Jerry Gana da Donald Duke


Jam’iyar SDP ta dakatar da yan takarar shugaban kasarta su biyu, Farfesa Jerry Gana da kuma tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Daraktan yada labarai na jam’iyar, Yemi Akinbode shine ya sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Talata a hedkwatar jam’iyar dake Abuja.

Ana zargin Duke da rashin girmama jam’iyar ya yin da shi kuma Gana aka zarge shi da kafa sabon shugabancin jam’iyar na kasa.

Gana da Duke sun shafe makonni suna iƙirarin kasancewa yantakarar shugaban kasa a jam’iyyar abin da ya kai su ga shiga kotuna a lokuta da dama.

Amma a ranar Alhamis jam’iyar ta amince da shugaban kasa Muhammad Buhari a matsayin dantakararta na shugaban kasa.

Jam’iyar ta bayyana cewa ta amince ta goyi bayan Buhari ne ganin yadda rikicin takarar shugaban kasa a kan yaki ci yaƙi cinyewa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like