Sauya sheka: Osinbajo ya gana da Akpabio


A jiya ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, sanata Godswil Akpabio a shirye-shiryen da sanatan yake na komawa jam’iyar APC.

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 03:06 na rana bisa rakiyar me bawa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Ita Enang.

Mutanen biyu sun zarce kai tsaye cikin ofishin mataimakin shugaban kasa dake fadar Aso Rock, manyan yan siyasar daga jihar Akwa Ibom sun isa fadar shugaban kasar ne sa’a guda bayan da shugaba Buhari ya tafi jihar Bauchi.

Ganawar ta su ta kawo karshe da misalin ƙarfe 5:20 na yamma.

Idan har ficewar tasa daga jam’iyar PDP ta tabbata to zai kasance sanata na biyu daga jihar, Anambra da ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar PDP.


Like it? Share with your friends!

-1
59 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like