Saudiyya Ta Soki Isra’ila Bisa Yadda Take Musgunawa Falasdiawa


Wakilin Saudiyya a zauren Majalisar Dinkin Duniya Abdul’aziz Al-Wasil ya yi jawabi a wajen taron Kwamitin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar inda ya mayar da martani da kakkausar murya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da take hakkokin Falasdinawa fararen hula.

Wasil ya ce, rufe hanyoyi da takunkumin da ake saka wa yankin Zirin Gaza ya saba wa doka da oda kuma abu ne mummuna na rashin tarbiyya kuma hakan ne yake janyo rikicin tattalin arziki da zamantake wa a yankin.

Wasil ya kara da cewa, Saudiyya ba za ta taba canja halayyarta ba ta neman a kawo karshen matsalar da Falasdinawa suke ciki kuma a kwai bukatar a samar da zaman lafiya mai dore wa amma kuma Isra’ila sai ta koma da yankunanta kamar yadda suke a shekarar 1967 sannan hakan za ta tabbata.

Wakilin na Saudiyya ya ci gaba da cewa, babu wani dalili da zai sanya Isra’ila da Falasdin su ci gaba da rikici, kuma akwai bukatar a yi aiki da dokokin kasa da kasa don kawo karshen rikicin ta hanyar kallon dauloli 2.

Ya kuma ce, Saudiyya a shirye ta ke ta ci gaba da bayar da goyon bayan dawo da zaman sulhu, kawo karshen mamayar da ake wa Falasdinawa sannan kuma daina zzaluntar su.

A karshe ya kuma yi nuni da idan aka ci gaba da mamayar Falasdin to a yi aiki da sashe na 7 na dokokin kwamitin kare hakkokin dana dam na Majalisar.


Like it? Share with your friends!

-1
96 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like