Saudiyya ta kirkiro wata manhajar tantance wa’azi


Hukumomi a Saudiyya na kirkirar wata manhajar wayar hannu wacce za ta sa ido kan wa’azuzzuka da addu’o’i a masallatai domin bai wa masu ibada damar sani idan mai wa’azi zai dade yana wa’azin.

Jaridar Al-Watan ta kasar Saudiyya ta ruwaito cewa Ministan harkokin musulunci na kasar Abdul Latif Al-Sheikh, ya bayyana cewa manhajar za ta bayar da damar sa ido a masallatai, kan tsawon lokaci da kuma ingancin wa’azuzzukan duk minti kuma duk dakika.

A baya dai, kasar Saudiyya, ta bar Malamai su yi waazinsu ba tare da katsalandan ba kan wa’azozi da makaloli wadanda tuni suka kai wasu ga zama ‘yan ta’adda, duk domin kokarin kautar da jama’a daga bin kasar Iran mai yada shi’anci.

A halin da a ke ciki, Saudiyya na duba batun kawo sauyi a koyarwar addini, kuma a na ci gaba da muhawara kan daidaita abubuwan da a ke wa’azi a kan su domin karkatar da mutane daga ra’ayin kasashen waje, ko na bangaranci ko kuma na kungiyar ‘yan uwa musulmi.

Ministan ya ce addini “ba fagen da za a rikita zukatan mutane bane, ko kuma a yi sagegeduwa ga tsaro da zaman lafiyar kasar nan mai albarka ba”.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like