Gamayyar Kungiyoyin Matasan jahohin Sokoto, Kebbi,Zamfara, sun gudanar zanga-zangar kin amincewa da dusa rundunar SARS da gwamnatin Najeriya tayi jiya Lahadi.

Da yake jawabi a madadin kungiyoyin, Cmrd Binji yace mun fito ne domin nuna rashin amincewar mu akan rasu rundunar SARS da akayi, domin mu a nan yankin Arewa mun san amfanin wannan runduna ta SARS, saboda suna aiki kamar yanda yakamata wajen yakar ‘yan ta’adda masu kissan al’umma da kuma garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.

Haka ma wadannan matasa sun yi kira ga kwamishinan ‘yan sanda na sokoto daya kai koken su ga shugaban ‘yan sanda na kasa domin mayar da rundunar SARS domin cigaba da ayukkan da take na kare al’umma da dukiyoyin su a jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da kuma Katsina.

A cikin nashi jawabi, Kwamishinna ‘yan Sanda na jahar Sokoto Ka’oji yayi godiya ga wadannan matasa akan sanin kansu da kuma nuna muhimmancin ‘yan Sanda a cikin al’umma.