Sarkin Kano ya samu kyakkyawar tarba a Ilorin


Sarkin Kano,Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu kyakkyawar tarba daga cincirindon jama’a a ziyarar da ya kai masarautar Ilorin.

Sarkin ya sauka a filin jirgin sama na birnin tare da rakiyar wasu mukarrabansa da misalin karfe 1:45 na rana.

Masu kadade da raye-raye sun samu damar shiga harabar filin jirgin inda suka yi masa maraba.

An ga matuka babura masu kafa uku na ta jigilar mazauna birnin ya zuwa filin jirgin saman domin su yi tozali da shi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like